1 Corinthians 8

Abincin da Aka Miƙa wa Gumaka

1To, game da abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa: Mun san cewa dukanmu muna da ilimi. Ilimi yakan kawo girmankai, amma ƙauna takan gina. 2Mutumin da yake tsammani ya san abu, sanin da yake da shi bai isa ba. 3Amma mutumin da yake ƙaunar Allah, Allah yana sane da shi.

4To, game da cin abincin da aka miƙa hadaya ga gumaka kuwa: Mun san cewa gunki ba kome ba ne a duniya, kuma babu wani Allah sai dai ɗaya. 5Gama ko da akwai abubuwan da ake ce da su alloli, a sama ko a ƙasa (don kuwa akwai “alloli” da “iyayengiji” da yawa), 6duk da haka a gare mu dai akwai Allah ɗaya kaɗai, Uba, wanda dukan abubuwa suke daga gare shi, wanda kuma saboda shi ne muke rayuwa, kuma akwai Ubangiji ɗaya, Yesu Kiristi, wanda ta wurinsa ne aka yi dukan abu, ta wurinsa ne kuma muke rayuwa.

7Amma ba kowa ne ya san wannan ba. Har yanzu, waɗansu mutane sun saba da tunani cewa gumaka ainihi ne, saboda haka saʼad da suka ci irin abincin nan, sukan ɗauka cewa kamar an miƙa wa ga gunki ne, kuma da yake lamirinsu ba ƙarfi, yakan ƙazantu. 8Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.

9Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ʼyancinku yǎ zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi. 10Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba? 11Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗanʼuwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yǎ hallaka. 12Saʼad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan. 13Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗanʼuwana yǎ yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yǎ yi tuntuɓe.

Copyright information for HauSRK